Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Cutar murar tsuntsaye ta ɓulla a Kano da wasu jihohi

Published

on

Hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC ta ce, cutar murar tsuntsaye ta bulla a jihohi bakwai na Arewacin kasar, ciki har da jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta rawaito shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu na bayyana hakan a jiya Talata.
A cewar sa, jihohin da cutar ta bulla sun hadar da, Kano da Bauchi, da jihar Plateau, sai kuma Gombe Nasarawa, da kuma jihohin Kaduna da Neja.
Shugaban ya ci gaba da cewa, ana kamuwa da cutar ne ta hanyar mu’amala da tsuntsayen da ke dauka da cutar, kuma ana iya yada ta, ta hanyar mutum da mutum idan ya yi tari ko atishawa.
Chikwe Ihekweazu yace, alamomin cutar na bayyana a cikin kwanaki biyu zuwa takwas, wanda suka hadar da mura da tari, ko sarkewar numfashi, da ciwon gabobi, har ma da ciwon kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!