Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Gwamnatin tarayya ta shawo kan matsalar lantarki
Ma’aikatar lantarki ta ƙasa ta ce ta shawo kan matsalar rashin wutar da aka fuskanta a farkon makon nan.
Ministan Lantarki Injiniya Abubakar D. Aliyu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar yau Asabar.
Sanarwar ta ce, an samu matsalar katsewar lantarkin ne sakamakon ƙarancin Gas da kuma ayyukan masu fasa bututun da ke samar da wutar lantarki.
Ministan ya ce, yanzu haka an gyara bututun Gas ɗin tashar lantarki ta Okpai da ke jihar Delta wadda wasu ɓatagari suka lalata.
Ta cikin sanarwar ministan ya yiwa ƴan Najeriya albishir da cewa, ana daf da kammala gyaran ƙarin tashoshin lantarki da aka dakatar da aikinsu saboda gyara daga lokaci zuwa lokaci.
Daga ƙarshe ministan lantarkin ya ce, Gwamnati na ci gaba da ɗaukar matakai ganin cewa ba a sake samun irin wannan matsalar ba a nan gaba.
Labarai masu alaƙa:
Buhari ya amince da kwangiloli 16 domin bunƙasa wutar lantarki
You must be logged in to post a comment Login