Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Sarkin Katsina ya kori Hakimi kan taimakawa Ƴan bindiga
Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ya kori ɗaya daga cikin hakimansa, sakamakon samun sa da hannu dumu-dumu wajen taimakawa ƴan ta’adda.
Masarautar Katsina bisa sahalewar Gwamnatin jihar ta tsige tare da korar Sarkin Fawar Katsina Hakimin Ƙanƙara Alhaji Yusuf Lawan.
Sakataren Masarautar Alhaji Bello Mamman Ifo ne ya tabbatar da hakan, a zantawarsa da wakilin Freedom Radio Yusuf Ibrahim Jargaɓa a daren Jumu’ar nan.
Ya ce, hakan ya biyo bayan kammala bincike da kwamitin da masarautar ta kafa yayi a kan hakimin.
Alhaji Bello Mamman ya ƙara da cewa, binciken da aka yi ya tabbatar da ƙorafe-ƙorafen da aka yi a kan hakimin, na yin haɗin kai da ƴan bindiga.
Yanzu haka dai tuni Masarautar Katsinan ta fara shirin domin maye gurbin sa a cewar sakataren.
Jihar Katsina dai na cikin jihohi Arewa da ke fama da matsalar ƴan bindiga masu garkuwa da mutane.
You must be logged in to post a comment Login