Labarai
Da dumi-dumi: kotu ta yankewa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa

Babbar kotun jihar Kano Mai lamba biyar ta yanke hukuncin kisa ga malamin nan Abdulmalik Tanko sakamakon kama shi da laifin kashe dalibarsa Hanifa Abubakar.
Kotun ta yanke hukuncin ne a zamanta na yau Alhamis karkashin jagorancin Mai shari’a Usman Na’abba.
Kotun ta yanke hukuncin kashe shi ne ta hanyar rataya da kuma zaman Shekaru 5 a gidan ajiya da gyaran Hali.
Haka kuma n yankewa wanda ake zargi da hannu a kisan nata su biyu Hashimu Isyaku da Fatima Jibril hukuncin kisa ta hanyar rataya da zaman shekaru biyu a gidan ajiya da gyaran hali.
You must be logged in to post a comment Login