Labarai
Hukuncin kotu kan sakin Sanusi II
Wata babbar kotu a birnin tarayya Abuja, yau jumma’a ta bada umarnin a gaggauta sakin tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi, da aka tura garin Awe, dake jihar Nassarwa.
Mai sharia’a Anwuli Chikere, ya bada umarnin bayan da mai shigar da kara Lateef Fagbemi, mai mukamin (SAN), ya nema.
Mai shari’a Chikere, ya kuma umarci da a gaggauta sakin tsohon sarkin ba tare da wani bata lokaci ko gindaya wasu sharuda ba.
Karar da tsohon sarkin ya shigar ta hada da babban sufeton ‘yan sanda na kasa, Muhammed Adamu; sai shugaban hukumar jami’an tsaro na farin kaya DSS, Yusuf Bichi; babban mai shari’a ministan sharia’a na kasa Abubakar Malami, da kwamishinan sharia’a na jihar Kano, Ibrahim Muktar, wand sarkin ya zarge su da hannu wajen tsare shi ba bisa doka ba.
Mai shari’a Anwuli Chikere, ya sanya ranar 26 ga watan Maris din da muke ciki don cigaba da saurarar karar.
You must be logged in to post a comment Login