Labaran Kano
Da mu za’a kawo karshen shaye-shayen miyagun kwayoyi –ALGON
Kungiyar kananan hukumomin ta jihar Kano ALGON ta ce ta shiga sha’anin yaki da matsalar shaye-shaye ne don bada ta su gudunmawa, a kokarin ta na kawo karshen matsalar a tsakanin matasan kasar nan.
Shugaban kungiyar Alhaji Lamin Sani ne ya bayyana hakan a yau, jim kadan bayan kammala shirin Barka da hantsi na nan tashar freedom radiyo, wanda ya mayar da hanakli kan kudirin kungiyar kananan hukumomin jihar Kano na yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Alhajin Lamin Sani ya kuma ce, idan har ana son cimma nassara kan yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi a nan Kano dama kasa baki daya, to kamata ya yi al’umma su hada hannun da gwamnatoci da kungiyoyi don magance matsalar.
Ya kara da cewa, dole ne iyaye su dauki gabarar daukewa ‘ya’yansu bukatun su na yau da kullum da kuma samawa ‘yara sana’o’in dogaro da kai, wanda hakan shi ne mataki na farko na dakile matsalar shaye shaye.
Labarai masu alaka:
Zamu dau matakan kare hakkin ma’aikata -Hadakar kungiyar masana’antu
Covid -19:Kungiyar likitocin dabbobi ta bada tallafi
Lamin Sani ya kuma ja hankulan matasan da su samarwa kansu sana’o’In dogaro da kai don rage zaman kashe wando, wanda hakan ne ke basu damar yin ta’ammali da miyagun kwayoyi.
You must be logged in to post a comment Login