Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Daga kasuwar musayen ‘yan wasa a nahiyar turai

Published

on

 

Kungiyar Kwallon kafa ta Inter Milan , na son zaman dan wasan gaban ta Lautaro Martinez , wanda Barcelona ke zawarci.

Martinez dan kasar Argentina, Barcelona na neman sa don mai da gurbin Luis Suarez , sai dai Inter Milan taki yarda a dai daita sakamakon son zaman dan wasan a kungiyar, kamar yadda Jaridar Sky Sport Italia ta ruwaito.

Haka zalika jaridar Calciomercato , ta ruwaito cewar Inter Milan, na son daukar dan wasan Real Madrid mai wasa a kungiyar Borussia Dortmund dan kasar Morocco Achraf Hakimi, sai dai zata fuskanci kalubale daga PSG, Bayern Munich da Chelsea.

Jaridar the Times , ta ambato cewar Chelsea na shirin sai da dan wasan tsakiyar ta dan kasar Faransa Ngolo Kante , don samun kudin cefanen ‘yan wasa, inda ake sa ran cewar Real Madrid na kan gaba wajen zawarcin dan wasan.Chelsea dai na son daukar ‘yan wasa Kai Harvetz da Ben Chilwell daga kungiyoyin Leverkusen da Leicester City .

Abinda ya sa Ganduje ya haramta yin goyo a babur

Rahoto : Nazari kan wasanni na gida tana ketare

Napoli kuma ta cimma matsaya da dan wasan baya dan kasar Brazil Gabriel Magalheas , kamar yadda jaridar Footmercato ta ruwaito ,sai dai dan wasan ana alakanta shi da Everton da Tottenham .

Ya yinda Sky Sport Italiya ta ruwaito ta hannun fitaccen dan jaridar nan Gianluca Di Marzio, kungiyoyin Fiorentina da Everton na gogayya da Ac Milan wajen daukar mai tsaron baya Thiago Silva, da zai bar PSG.

Kungiyar Ac Milan , ta sanar dacewa , mai yiwuwa dan wasa Naby Keita , ya koma kungiyar daga Liverpool.

Jaridar Telegraph, ta ruwaito cewar kungiyar Bayern Munich na shirin sai da dan wasa David Alaba, wanda hakan ya sa kungiyoyin Liverpool , Manchester City da PSG zama cikin shirin ko ta kwana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!