Labarai
Dakarun haɗin gwiwa na ƙara kaimi wajen yaƙi da ’yan bindiga a Borgu

Jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun ƙara kaimi wajen yaƙi da ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Borgu da ke Jihar Neja, bayan samun rahotannin cewa masu laifin na tilasta wa mazauna wasu ƙauyukan Dakera karɓar kuɗi domin sayo musu kayan abinci da sauran buƙatun yau da kullum.
Rahotanni sun nuna cewa bayan samun bayanan sirri kan wannan sabon salo da ’yan bindigar ke amfani da shi wajen samun kayan masarufi, jami’an tsaro suka ƙaddamar da samame a yankin tare da tsaurara matakan tsaro domin hana ci gaba da wannan aiki.
A yayin aikin, jami’an tsaron sun yi nasarar cafke wasu da ake zargi da hannu wajen taimaka wa ’yan bindigar samun kayan masarufi, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu a lamarin.
Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa za su ci gaba da matsa wa masu aikata laifuka lamba tare da katse duk wata hanyar da za ta ba su damar samun tallafi daga al’umma.
Mazauna yankin sun yaba da matakin da jami’an tsaro suka ɗauka, suna mai fatan hakan zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da matsalar ta fi kamari.
You must be logged in to post a comment Login