Labarai
Gwamnatin Zamfara ta sha alwashin ci gaba da haɗa kai da dakarun tsaro don magance ta’addanci

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sake jaddada kudirinta na kara hada kai da Rundunar Sojin Sama kasar nan da sauran hukumomin tsaro domin magance matsalar rashin tsaro a jihar.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Muhammad Mahmud Dantawasa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aya fitar inda ya ce Gwamna Dauda Lawal na ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya ta fuskar kayan aiki da hadin gwiwa domin dawo da zaman lafiya a fadin jihar.
Ya ce ziyarar da gwamnan ya kai wa jami’an Rundunar Sojin Sama da ke filin jirgin saman Gusau kwanan nan na da nufin kara musu kwarin gwiwa a yakin da suke yi da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a yankin Arewa maso Yamma.
Dantawasa ya bayyana Rundunar Sojin Sama a matsayin muhimmiyar abokiyar aiki wajen yaki da rashin tsaro, yana mai cewa hare-haren sama da bayanan sirri da rundunar ke samarwa sun taimaka wajen tarwatsa ayyukan masu laifi a yankunan karkara.
Kwamishinan ya nuna fatan cewa ci gaba da hadin gwiwa tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro zai taimaka wajen inganta tsaro da dawo da kwarin gwiwar al’umma a jihar.
You must be logged in to post a comment Login