Labarai
Duk wanda gwamnati ta yi wa auren gata ba zai saki matar ba sai ya zo gabanmu- Daurawa

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa duk wanda zai ci gajiyar shirin auren gata da gwamnatin jihar ke shirin gudanarwa, ba zai iya raba aurensa ba sai bayan ya koma gaban hukumar domin sasanta matsalolin da suka taso.
Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a wani ɓangare na shirye-shiryen auren gata na mutane 3,000 da gwamnatin jihar Kano ke shirin yi.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce gwamnatin jihar na kashe kuɗi masu yawa wajen tallafa wa ma’auratan, don haka tana fatan auren zai dore ba tare da saurin rugujewa ba inda ya ce duk wanda yake son rabuwa da matarsa saboda wata matsala dole ne ya gabatar da ƙorafinsa ga Hisbah tun da a ƙarƙashin kulawarta aka daura auren.
Ya ƙara da cewa shirin auren gata na bana zai tallafa wa ma’aurata da kayan ɗaki, kayan aure, kayan abinci da kuma tallafin kuɗi domin rage wa marasa galihu wahalar da ke tattare da yin aure.
Hukumar Hisbah ta kuma bukaci ma’auratan da za su ci gajiyar shirin da su riƙe aurensu da muhimmanci tare da yin haƙuri da juna domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidajensu.
You must be logged in to post a comment Login