Connect with us

Labarai

Dakarun Operation Fansan Yamma sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a Kaura Namoda

Published

on

Dakarun sojin kasar nan na Operation Fansan Yamma, sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a ƙauyen Unguwar Rogo, a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara.

Rundunar ta ce sojojin sun ceto fararen hula tara, ciki har da jariri, bayan ’yan bindiga sun yi wa mutanen da ke tafiya a wata hanya kwanton bauna.

Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce ’yan bindigar sun buɗe wa motocin da ke wucewa wuta daga cikin wata gonar gero, da nufin yin garkuwa da mutanen da ke cikinsu.

Ya ce sojojin da aka aika wurin bayan samun kiran neman agaji sun yi artabu da ’yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji.

A cewar rundunar, mata biyu sun samu raunukan harbin bindiga a yayin harin, kuma an kai su asibiti domin kula da lafiyarsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!