Connect with us

Labarai

Jam’iyyar APM ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomi 20 a Bauchi

Published

on

Jam’iyyar APM mai alamar Rogo ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 20 a zaben da aka gudanar a Jihar Bauchi ranar Litinin.

Shugabar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi, BASIEC, Jummai Abubakar, ce ta sanar da sakamakon zaben a daren Litinin. Ta ce APM ta kuma lashe kujerun kansiloli 319.

Sai dai jam’iyyun SDP, NRM, ZLP da YPP sun samu kujerar kansila daya kowannen su.

 

Tun ranar Lahadi ne wasu jam’iyyun adawa suka sanar da kauracewa zaben, suna zargin an shirya shi ne domin fifita APM.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana zaben a matsayin wanda aka gudanar cikin lumana, yana mai cewa kauracewar wasu jam’iyyun ba za ta rage sahihancinsa ba. Gwamnatin jihar ta kuma ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu domin bai wa ma’aikata damar kada kuri’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!