Connect with us

Labarai

Rundunar Operation Fansan Yamma ta dakile yunkurin sace mutane tare da ceto mutum 14 da ke tsare

Published

on

Rundunar Sojin kasar nan ta Operation Fansan Yamma, ta dakile wani yunkurin sace mutane, tare da ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

 

Rundunar ta gudanar da aikin ceton a yau , bayan samun sahihin bayanan sirri kan wasu mutane da ake zargin suna aikata laifuka a kusa da kauyen Magazu.

 

Bayan samun bayanan sirrin , sojojin sun isa yankin inda suka yi arangama da wasu ‘yan bindiga da ake zargin suna kokarin yin garkuwa da fararen hula, ciki har da masu ababen hawa.

 

Sojojin sun bude wuta kan ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu barin motarsu tare da tserewa zuwa cikin daji.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!