Labarai
Daliban Sudan sun bukaci gwamnatocin Kano da Jigawa su yi koyi da gwamna El-Rufa’i
Kungiyar dalibai ‘yan Najeriya da ke karatu a kasar Sudan, ta yi kira ga gwamnatocin juhohin Kano da Jigawa da kan su yi koyi da gwmanatin jihar Kaduna kan yunkurin da take na dawo da dalibanta da suke karatu a Sudan domin magance musu matsalolin da suke fuskanta.
Dakta Abdulmudallif Ahmad Muhammad wanda mamba ne a kungiyar daliban, kuma Malami a kwalejin nazarin addinin musulunci ta Legal da ke Daura a jihar Katsina, ne ya bukaci hakan, yayin tattaunawarsa da Freedom Radio da safiyar yau, kan halin da daiban Najeriya ke ciki a kasar Sudan dama makomar su idan suka dawo gida.
Dakta Abdulmudallif Ahmad Muhammad ya kuma ce, hatta abincin da daliban za su ci, sai iyayansu sun tura musu da kudi ta asusun wani dan kasar Sudan, sannan ya isa gare su don su yi amfani da shi.
You must be logged in to post a comment Login