ilimi
Daliban Yanzu na sakaci da Karatu – Kungiyar Dalibai
- Kungiyar ta ce ilimi shike gina rayuwar dan Adam
- Ta bayar Tallafin Kayayyakin karatu
- Tayi kira ga daliban da su maida hankali wajen samun ilimi ingantacce.
Mai bada shawara kan harkokin shari’a a kungiyar tsoffin daliban Jami’ar Bayero ta Kano aji na 1992, Barista Sa’idu Muhammad Tudunwada ya koka game da sakacin dalibai a harkokin karatun su.
Barista Sa’idu ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilin Freedom Radio Nura Bello da safiyar yau.
Ya ce ‘kungiyarmu na bayar da gudunmawar kaya da kuma da tallafin karatu ga dalibai marasa karfi’.
A nasa bangaren Mudi Adamu wanda mamba ne a kungiyar, ya ce “muna tallafawa abokan karatunmu wadanda suke cikin matsala da ma wadanda suka rasu kuma iyalansu suna bukatar tallafi.”
Kungiyar ta yi kira ga dalibai da su mayar da hankali wajen koyon ilimi mai inganci don gina rayuwarsu.
You must be logged in to post a comment Login