Labarai
Dalibin Jami’ar Bayero ya lashe gasar gwarzo tarihi na Afrika
Wani dalibi Abdulmalik Abubakar Isa dan asalin jihar Kano wanda yake karantar harkokin shari’a a jami’ar Bayero a Kano ya sami nasarar zama gwarzon shekara a gasar tarihi ta Afrika da aka fafata karon karshe a babban birnin tarayya Abuja.
Kuma aka nadashi sarautar gwarzon tarihin Africa “Keeper of African History 2023”.
Dalibin ya fafata a gasar ne ta kimamin dalibai 2,345 na dukkan Jami’o’in Nigeria inda ya sami nasarar tsallake matakai daban-daban har suka dawo su talatin, wanda kowace shiyya ta kasar nan ta sami wakilcin mutane biyar-biyar.
Bayan fafata matakin ne suka dawo su biyu a kowace shiyya wanda ya sami nasarar fitowa daga Jami’ar ta Bayero a matakin.
Sun tsallaka zuwa matakin gwabzawa a tsakanin shiyyoyi inda ya nasarar fitowa a cikin mutane shida kachal. Wanda suka rankaya babbar Jami’ar tarayya ta Calabar dake Birnin Cross River inda ya sami nasarar fitowa a cikin mutane hudu zakarun da zasu tsallaka matakin kusa dana karshe.
Bayan nan Jami’ar Bayero ta karbi bakuncin matakin kusa dana karshe inda yayi nasarar tsallakawa matakin karshe tare da abokin karawarsa daya fito daga jami’ar Ilorin dake jihar Kwara.
Bayan fafata zagayen karshe a Jami’ar Nile dake Abjua, ya sami nasarar zama gwarzon gasar inda ya sami nadin sarautar “Gwarzo kuma mairike da kambun tarihin Africa na shekarar 2023”
Dalibin ya samu kyaututtuka daya hada da tsabar kudi naira Dubu dari biyar, an biya masa zuwa kasar Kenya domin yawon shakatawa, Samun kambun zama “Gwarzon Tarihi na Africa” da sauran kyaututtuka.
Dalibin ya bayyana matukar farincikinsa da godiya ga Allah bisa nasarar daya bashi duk da cewa ba fannin tarihi yake karanta ba, amma tunda gasar ta ƙunshi dukkan dalibai dake karantar kowane fanni, hakan ya bashi damar zama zakara a gasar.
Daga karshe yayi kira ga sauran dalibai da su maida hankali su kara jajircewa domin komai mai iya yiwuwa ne a fannin ilimi.
Ya kara da cewa “duk da ina shugaban dalibai masu karantar Shari’a ta Jami’ar Bayero, gashin kuma ina shekarar karshe inda nake kokarin kammala nazarin bincike wato (project), harda ma shugabancin dalibai na mazabata, wato Kaura Goje Students’ Association (KAGSA) dake karamar hukumar Nasarawa, hakan bai hanani jajircewa da maida hankali wajen fadada bincike ba.”
Ya kammala da godewa Allah tare da fatan sauran dalibai zasu dage wajen maida hankali a karatuttukansu baki daya.
Daga bisani itama Jami’ar Bayero ta Karramani da lambar yabo, da ta Alumni, da Kudi naira Dubu dari biyu da hamsin (250,000.00) wanda wanda shugaban jami’ar Farfesa Sagir Abbas ya Mika masa
You must be logged in to post a comment Login