Labarai
Dalilan da ya sa Ganduje ya rufe masallacin Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara a Kano
Sakamakon rahotanni da aka samu dangane da kalaman na tunzura Jama’a da ka iya kawo tashin hankali da sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke yi majalisar zartarwar Kano ta umarci da a gaggauta rufe masallaci da cibiyar da yake gudanar da karatukansa a filin mushe da ke nan Kano.
Ka zalika Majalisar zartarwa ta Kano ta ce sai jami’an tsaro sun kammala binciken da suke gudanar wa a halin yanzu kan malamin bisa furta kalaman tunzura jama’a a ya yin da yake gudanar da wa’azi a masallacin sa.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya bayyana hakan a daren jiya a fadar gwamnatin Kano ya yin da yake zantawa da manema labarai.
Malam Muhammad Garba ya kara da cewa, majalisar zartarwa ta Kano ta kuma umarce shi sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da ya dakatar da wadannan wa’azi da yake yi wanda ka iya kawo rudani da tashin hankali a nan Kano da ma kasa baki daya.
Majalisar ta kuma umarci kafafen yada labarai dana sada zumunta da su dakatar da sanya karatuttukan sa don tabbatar da samun zaman lafiya a jihar Kano
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa, gwamnatin ta Kano ta kuma umarci jami’an tsaro da daukar matakin gaggawa kan duk mai irin wadannan kalaman anan Kano.
You must be logged in to post a comment Login