Labarai
Dalilan da suka sanya gwamnatin Kano daukar alarammomi aikin koyar wa – Ganduje
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da daukan alarammomi sittin da za su koyar a makarantu goma sha biyar da gwamnatin ta samar don koyar da almajirai ilimin zamani.
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya amince da hakan a jiya Litinin.
Amincewar ta biyo bayan karbar rahoto daga hukumar da ke kula da makarantun Isalamiyya a jihar Kano, karkashin jagorancin kwamishinan Ilimi Malam Muhammad Sunusi Kiru.
Gwamna Ganduje ya ce, gwamnatin sa ta samar da kwamitin da zai magance matsalar hana barace-barace a kan titinan jihar Kano, wanda kuma ta tsara samar da makarantun da za su bai wa almajiran damar hadar Alqur’ani mai da na zamani don kyautata rayuwarsu.
Idan dai za a iya tunawa gwamnatin ta samar da makarantun a kananan hukumomin Bunkure da Madobi da Bagwai da kuma sauran kananan hukumomi goma sha biyu cikin kananan hukumomin Arba’in da hudu na fadin jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login