Labarai
Abin da ya sanya Majalisar dinkin duniya ta ce an kashe manoma 110 a Borno
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kimanin mutane 110 aka kashe a harin da ake tunanin ƴan Boko Haram ne suka kai wa manoma a jihar Borno.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai kula da ayyukan jin-ƙai na Majalisar Edward Kallon ya fitar, inda ya kira harin da mummunan tashin hankali.
Sai dai sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar bayan jana’izar mutanen, ta ce mutane 43 ne suka hallaka a harin.
Bayan kisan, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi kira ga matasa da su shiga aikin ƴan banga ko sa-kai domin yaƙi da ta’addanci.
A ranar Asabar ne aka samu rahotannin da ke cewa wasu da ake tunanin mayaƙan Boko Haram ne sun shiga gonaki inda suka kashe fiye da mutum 40.
Lamarin ya faru ne a yankin Koshebe na Zabarmari da ke cikin Ƙaramar Hukumar Mafa ta jihar Bornon.
You must be logged in to post a comment Login