Labarai
Dalilin da ya sa ƙungiyar ƙwadago ta kasa (NLC) ta janye yajin aiki a Kaduna
Ƙungiyar ƙwadago ta kasa (NLC) ta janye yajin aikin kwanaki biyar (5) da ta fara a jihar Kaduna
Tun farko dai gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon ƙarkashin jagorancin shugaban ƙungiyar NLC Ayuba Wabba sun jagorancin ma’aikata a jihar ta Kaduna wajen gudanar da zanga-zangar adawa da salon da gwamna El-Rufai ya dauka na korar ma’aikata.
Tun farko dai gwamna Nasir El-Rufai ya ƙalubalanci ƴan ƙwadagon da cewa zanga-zangar da suke yi da yajin aikin ba zai sa gwamnatin jihar ta sauya matsayinta kan batun ba.
Sai dai da ya ke zantawa da manema labarai a daren jiya laraba shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) kwamared Ayuba Wabba ya ce ƙungiyar ta janye yajin aikin da ta fara.
Ya ce sun dau wannan mataki ne ganin cewa gwmanatin tarayya ta dau alkwarin shiga tsakanin don sasanta ɓangarorin biyu
You must be logged in to post a comment Login