Kaduna
Dalilin da ya sa muka dakatar da Kwankwaso daga jam’iyya – PDP
Jam’iyyar PDP ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso tana mai zargin sa da hannu a rikicin da ya faru a yayin zaben shugabannin shiyyar arewa maso yamma wanda ya gudana a garin Kaduna a makon jiya.
Bayanin dakatarwar na kunshe ne cikin wata wasika da tsagin jam’iyyar da ke biyayya ga tsohon ministan kasashen wajen kasar nan Ambasa Aminu Wali, ya fitar.
Takardar dakatarwar na dauke ne da sanya hannun sakataren tsagin shugabancin da ke biyayya ga Aminu Wali, H. A Tsanyawa.
Rahotanni sun ce jam’iyyar PDP a jihar Kano dai ta dare gida biyu, inda daya bangaren shugabancin ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, yayin da daya bangaren ke biyayya ga Aminu Wali.
A yayin taron zaben sabbin shugabannin shiyyar arewa maso yamma da ya gudana a garin Kaduna a ranar asabar ta makon jiya, an yi ta bata kashi tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar wanda ya kai ga farfasa akwatunan zabe da takardun kada kuri’a.
You must be logged in to post a comment Login