Connect with us

Siyasa

Dan takarar shugaban kasa a ADP ya yi gargadi kan yunkurin sauya sunansa

Published

on

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) a zaben 2027, Ambasada Aliyu Bin Abbas, ya yi gargadi kan duk wani yunkuri na sauya sunansa a matsayin dan takarar jam’iyyar ba tare da bin ka’idojin doka ba.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Okpani Jacob Onjewu Dickson, ya fitar a Kaduna ranar Juma’a, Abbas ya ce duk wani yunkuri na boye don janye ko maye gurbinsa zai zama barazana ga dimokuradiyya da kuma hakkin magoya bayan jam’iyyar.

Ya ce ya samu bayanai kan matsin lambar siyasa da ake zargin ana yi wa shugaban jam’iyyar ADP na kasa, Injiniya Yabagi Yusuf Sani, domin a sauya sunansa domin samar da dan takara guda daya daga Arewacin Najeriya.

Abbas ya jaddada cewa ya samu tikitin takarar ne ta hanyar da kundin tsarin mulkin jam’iyyar da dokokin zabe suka tanada, yana mai cewa tikitinsa ba wata kadara ba ce da za a yi ciniki da ita a bayan fage.

Dan takarar ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su kare martaba da mutuncin ADP tare da tabbatar da cewa an adana dukkan takardun da suka shafi zaben fidda gwani da kuma sadarwa da hukumar INEC ba tare da yin wani sauyi ba sai bisa ka’ida.

Ya kara da cewa dimokuradiyyar Najeriya ba za ta zama abin da za a yi amfani da ita domin biyan bukatun mutum ko wasu kungiyoyin siyasa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!