Siyasa
Zamu nemi hakkin zaluncin da aka yi mana a Gombe na takarar gwamna – Pantami

Tsohon Ministan Sadarwa na kasa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya zargi jam’iyyar APC a jihar Gombe da karya dokoki wajen tsayar da dan takarar gwamna domin zaben 2027.
Pantami ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da BBC suka wallafa, inda ya ce tsarin consensus da aka bi wajen fidda dan takarar ya nuna bangaranci.
A cewarsa, an fifita bangaren Jamil Isyaku Gwamna ta hanyar ba shi tikitin takarar gwamnan jihar, abin da ya sabawa ka’idojin jam’iyyar.
Haka kuma, Pantami ya bukaci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da su sanya ido kan lamarin tare da daukar matakin da ya dace
You must be logged in to post a comment Login