Connect with us

Labarai

Matatar Dangote ta kara farashin mai da Naira 85 kan kowace lita

Published

on

Matatar man fetur ta Dangote ta kara farashin mai da Naira 85 kan kowace lita, inda ta daga farashin sayar da litar man daga Naira 1,265 zuwa Naira 1,350 a matakin sayar da mai ga ’yan kasuwa.

 

Karin farashin, wanda ya kai kusan kashi 6.7 cikin 100, na zuwa ne a daidai lokacin da farashin danyen mai ke ci gaba da karuwa a kasuwannin duniya.

 

Sabon farashin na Dangote ya haura kudin da ake hasashen shigo da litar man fetur cikin kasar nan, wanda ya kai kusan Naira 1,311.

 

Wannan na iya yin tasiri wajen kara sauya farashin man fetur a gidajen mai na ’yan kasuwa masu zaman kansu.

 

Tuni dai wasu gidajen mai suka fara sauya farashin man nasu, sakamakon wannan karin.

 

A kasuwannin duniya kuwa, farashin danyen mai na Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma’aunin farashin danyen man Najeriya, ya karu da kashi 2.8 cikin 100, inda ya haura dala 100 kan kowace ganga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!