Labarai
DMO ta ce kaso 73.5% na kudaden shigar Nijeriya a bana za’ayi amfani dasu ne wajen biyan bashi
Ofishin kula da basuka na DMO ya gargadi gwamnatin Nigeria game da karbo bashi a nan gaba, inda ya bayyana cewa kashi 73.5% na kudaden shigar kasar a bana za’ayi amfani dasu ne wajen biyan bashi.
Ofishin kula da basukan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa bashin da ake bin kasarnan na iya kaiwa kasha 37.1% na jimillar arzikin da take samu a cikin gida wato GDP a bana, daga kasha 23% da aka samu a bara.
Ko a watan jiya ma majalisun dokokin kasarnan said a suka amince da wasu makudan kudade da suka kai naira Tiriliya 22.7 kwatankwacin dala dubu 50 daga babban bankin Nigeria na CBN kwanaki 30 gabanin karewar gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Jimillar bashin da ake bin Nigeria dai ya kai dala biliyan 103 kwatankawacin naira tiriliyan 46 ya zuwa watan Disambar bara.
Rahoton: Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu
You must be logged in to post a comment Login