Labarai
Dokar tsaftar muhalli a gobe bata shafi dalibai masu rubuta WAEC ba – Kabiru Getso
Gwamnatin jihar Kano ta sahalewa Daliban dake rubuta Jarabawar kammala Sakandire ta yammacin Afrika WAEC fita a gobe asabar duk da cewa za a gudanar tsafatar muhalli a fadin jihar Kano.
Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake jawabi bayan kammala gudanar da duban tsaftar muhalli na kasuwanni da hukumomin gwamnati har ma tashoshin mota da ake gudanarwa a karshen kowanne wata.
Ya ce, ma’aikatar muhalli ta samar da wata shaidar da za a rabawa jami’an da ke sintirin raba kayan jarrabawar da kuma malaman da ke kula da rubuta jarrabawar ta yadda za su nuna a matsayin shaida a gobe don basu damar zuwa cibiyoyin rubuta jarrabawar.
Dakta Getso, ya kuma ce dalibai kuwa kayan makarantar su da kuma katin jarrabawar su zai zamo shaidar da za su fita a gobe asabar don rubuta jarrabawar.
Sai dai ya bukaci wadanda aka sahalewa dokar da su yi amfani da lokacin wajen isa guraren da wuri don baiwa jami’an tsaftar muhalli damar gudanar da ayyukan su.
You must be logged in to post a comment Login