News
DSS ta ci gaba da tsare matashin nan Baffa Hotoro a hannunta
Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya DSS a jihar Kano ta ci gaba da tsare matashin nan Baffa Hotoro bayan ya wallafa bidiyon neman afuwa ga Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da ya yiwa zagin tsamar nama.
Bayanan da Feedom Radio ta samu sun tabbata da cewa hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe da dama a kan matashin ciki har da na Gwamnatin Kano kan zargin yin kalaman ɓatanci.
Hukumar ta kuma karɓi ƙorafin iyalan Sheikh Ɗahiru Bauchi kan zagin da ya yi masa, kuma shi ne ma aka kammala a jiya har ya nemi afuwa.
Hukumar zata dauki mataki na gaba kan zarge-zargen da ake yi masa.
Rahoton: Bashir Sharfadi
You must be logged in to post a comment Login