Connect with us

Labarai

EFCC na shirin ɗaukaka ƙara kan shari’ar Abubakar Malami

Published

on

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC, Ola Olukoyede, ya ce hukumar za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya soke ƙwace wasu kadarori tara da ake dangantawa da tsohon Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami.

 

Olukoyede ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake gabatar da jawabi a wani taro da aka yi a Jami’ar Cambridge da ke Birtaniya.

 

Ya ce EFCC ta gano kadarori 57 da ake dangantawa da Malami, inda kotu ta amince da ƙwace 48 daga cikinsu, yayin da kotu ta yi watsi da bukatar ƙwace sauran tara da ke jihohin Kebbi da Kaduna.

 

Olukoyede ya ce hukumar za ta ɗaukaka ƙara domin ƙoƙarin kwace sauran kadarorin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!