Connect with us

Labarai

NCCS ya fara gudanar da taron kwanaki biyu a Kano

Published

on

Kwamitin tuntuɓa da Shawarwari na Ƙasa kan harkokin Ƙididdiga, ya fara gudanar da Taron mambobinsa na kwanaki biyu a nan Kano.

 

Taron wanda aka yi wa take da: “Buɗe fa’idodin bayanai domin ci gaban ƙasa: inganta ƙididdigar bayanan hukumomi da kuma tafiyar da mulki bisa dogaro da bayanai.”

 

Da ya ke jawabi yayin taron shugaban hukumar Ƙididdiga ta ƙasa NBS Prince Adeyemi Adeniran, ya ce, gudanar da irin wannan taro na taimakawa wajen ƙara ingantawa da kuma ƙara ƙaimi wajen adana muhimman bayanai da ke ƙara inganta ci gaban ƙasa. 

 

Ya ce, ”Najeriya na bukatar tsarin kididdiga na zamani wanda zai iya sauya bayanai daga mabambantan hanyoyi zuwa sahihan hujjoji da za su taimaka wajen yanke shawara da kuma bunkasa kasa, aikinta bai tsaya ga samarwa da wallafa kididdiga kadai ba, mu na kuma yin kokarin gina tsarin kididdiga na zamani da zai dace da sauye-sauyen duniya da kuma bukatun masu amfani da bayanai.”

 

”Najeriya ta shiga wasu tsare-tsaren kasa da kasa da domin karfafa tsarin kididdiga mai inganci da hada kowanne bangare, a watan Disamba mai zuwa na shekara nan ne za mu karbi bakuncin taro karo na 20 na kwamitin Daraktocin hukumomin kididdiga na kasashen Afirka, CoDGs.”

 

A tarihi wannan zai zama karo na farko da Najeriya ta karbi bakuncin irin wannan muhimmin taro, wanda alama ce ta kara girman rawar da kasar ke taka wa a fannin kididdiga a Afirka.

 

Haka kuma ta cikin jawabin nasa, shugaban na hukumar kididdiga ta Najeriya NBS, Ya kuma yi kira ga dukkan hukumomin gwamnati na tarayya da jihohi da su hada kai wajen sabunta tsarin kididdiga, inganta bayanan hukumomi da kuma tabbatar da cewa ana amfani da bayanai wajen yanke shawara.

 

A nasa jawabin, gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya yaba wa masana a fannin ilimin ƙididdiga, inda ya ce, su na taka muhimmiyar rawa musamman a fannin ankarar da gwamnati kan irin ababen more rayuwar al’umma. 

 

Ya ce, ”Ya zama wajibi mu yaba wa wadannan mutane kwararru a fannin kididdiga, saboda su na taimakawa kwarai da gaske wajen shaida wa gwamantoci irin bukatun mutane dangane da ababen more rayuwa da suke bukata.

 

Sai da gudunmawarsu ne ake iya gane abubuwan da ake so a aiwatar, idan ba haka ba gwamnati za ta iya zuwa yankin da ake bukatar makaranta ta gina asibiti, wurin da ake bukatar asibiuti kuma ta yi musu titi, amma ta hanyar aikinsu ne ake gane bukatun mutane”.

 

”Don haka gwamantin jihar Kano za ta ci gaba da ba su dukkan gudunmawar da ta dace wajen ganin cewa su na ci gabna da bai wa mutane gudunmawa su ma”

 

Taron dai, ya samu halartar masana a harkokin ƙididdiga daga faɗin Najeriya. 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!