Labarai
EFCC: ta gargadi ‘yan Najeriya da su guji bada gudunmawar karya
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gargadi ‘yan Najeriya da su guji yin alkawarin karya wajen bada taimakon kayayyakin da zasu taimaka wajen warkar da masu dauke da cutar COVID-19.
Mukadashin hukumar ta EFCC Ibrahim Magu yayi wannan gargadi ‘yan Najeriya cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar Mr Tony Orilade ya fitar a Abuja.
Ibrahim Magu ya ce akwai bukatar dake akwai a gargadi ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su guji amincewa da masu bada taimakon karya kasancewar akwai dokokin da ake bi wajen bada gudunmawa kan cutar COVID-19.
Akan haka ne shugaban hukumar ta EFCC ya kara da cewar, Gwamnatin tarayya ta sanar da asusun bankin da duk wanda yake da sha’awa wajen bada gudunmawa ko taimako da ya sanya a ciki kan yaki da cutar ta COVID-19.
You must be logged in to post a comment Login