Labaran Wasanni
El Clasico: Barcelona ta lallasa Real Madrid har gida
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ragargaji abokiyar hamayyarta Real Madrid da ci 4 da nema a gasar La Liga.
Fafatawar da itace wasan hamayya mafi daukar hankali a fadin duniya da akaiwa take da *El Clasico*.
Filin wasa na Santiago Bernabue da ke birnin Madrid shine ya karbi bakuncin wasan da ya gudana a ranar Lahadi 20 ga Maris din 2022.
Dan wasa gaban kasar Gabon Aubameyang ne ya zura kwallaye biyu a minti na 29 da 51.
Sai kuma dan wasa Ronald Araujo ya zura kwallonso a minti na 38 , kana shima Ferren Torres ya zura kwallo a minti na 47.
Har zuwa yanzu dai Real Madrid na matakin farko da maki 66 a wasanni 29 da ta buga.
Yayinda Barcelona ta ke a mataki na 4 da maki 54 a wasanni 28, wato akwai kwantan wasa guda daya da zata buga.
Kafin wannan wasan dai tin daga shekarar 2020 Barcelona ba tayi nasara akan Real Madrid ba.
Inda wasan karshe kafin na ranar Lahadin da Barcelona tayi nasara Real Madrid ta doke ta daci 3 da 2 wasan da ya gudana a ranar 12 ga watan daya na shekarar da muke ciki.
Kuma nasara ta farko da mai horarawa Xavi Hernandez ya yi akan Real Madrid a matsayin mai horarwa na Barcelona.
Amma Real Madrid ta buga wasan bata reda dan wasan gabanta da yafi kowa zura kwallo a gasar La Liga ba wato Karim Benzema sakamakon raunin da ya ke fama da shi.
You must be logged in to post a comment Login