Labarai
El-Rufa’i ya yi tir da kai hari tsakanin Zaria zuwa Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta yi tir da kai harin wasu ƴan bindiga sun tare kan titin Zaria zuwa Kaduna daura da makarantar horas da sojoji da ke Jaji cikin daren jiya.
A cewar Kwamishinan dake kula da tsaro da ala’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan lokacin da wakiliyar Freedom Rediyo Shamsiyya Haruna ke ganawa da shi ta wayar tarho da safiyar yau a cikin shirin ”An tashi lafiya” ya ce sun sami rahoton ‘yan bindigar sun bude wuta da misalin karfe 2 na dare akan motocin dake bin hanyar Zariya zuwa Kaduna.
Samuel Aruwan ya ce gwamnatin Kano ta bada umarnin da a baiwa wadanda abun ya rutsa da su kulawar gaggawa a asibitin 44 da ke Kaduna.
A cikin ‘yan kwanakin nan ayyukan ‘yan bindiga ya kara ta’azzara a jihar ta Kaduna.
Ko da a makon da ya gabata sai dai wasu masu garkuwa da mutane suka sace wasu ma’aikata a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.
Masu fashin baki kan al’amuran yau da kullum sun bayyana fargabar kan yadda ayyukan ta’addanci ke kara ta’azzara a yankin Arewacin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login