Labarai
El-Rufai zai fara raba magunguna ta hanyar amfani da jirage masu sarrafa kan su
Gwamna Nasir El-Rufai ya sanya hannu a wata yarjejeniya da wani kamfani, a wani mataki na raba magunguna a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na jihar Kaduna ta hanyar amfani da kananan jirage masu sarrafa kawunansu (drones) wanda aka yi yau.
A jawabinsa, Gwamna El-Rufai ya ce wannan kamfani da ke Kasar Amurka wanda ke da reshe a Kasar Ghana ya zabi Jihar Kaduna ne don ganin yadda jihar ta dauki sha’anin kiwon lafiya da muhimmanci.
Gwamnan ya kara da cewa, “ wannan tsari zai taimaka mana wurin rarraba magani da alluran riga-kafi zuwa duk lunguna da sakunan da ke jihar nan musamman inda muke fama da matsalolin tsaro kamar Birnin Gwari.
Sannan wannan tsarin zai taimaka mana wurin samar da ayyukan yi ga matasanmu tun da a nan Kaduna za su rika kera wadannan jirage masu sarrafa kawunansu”.
You must be logged in to post a comment Login