Labaran Wasanni
Everton ta gabadar da Lampard a matsayin sabon mai horarwa
Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta gabatar da Frank Lampard a matsayin sabon mai horar da tawagar.
Everton dai ta sanar da hakane a ranar Litinin 31 ga Janairun 2022, wanda ya amince da sanya hannu a kwantaragin shekaru biyu da rabi.
Lampard tuni ya kasance a filin wasan kungiyar tin bayan da ya kasance ba shida kungiyar da ya ke jagoranta tsahon shekara guda.
Tsohon dan wasan kasar Ingila zai fara jagorantar
Everton a ranar Asabar mai zuwa a wasan da zasu kece raini da Brentford a wasa zagaye na hudu a gasar FA Cup.
Mai shekaru 43 ya maye gurbin mai rikon kwarya na kungiyar Duncan Ferguson da kuma Vítor Pereira wadanda suka jagoranci kungiyar a baya.
Kawo yanzu dai Lampard zai ci gaba da jagorantar Everton wadda maki hudu ne kacal tsakaninta da kungiyar da ke shirin fadawa a ji na biyu a gasar Firimya.
Haka kuma Lampard zai zama mai horarwa na bakwai cikin shekaru shida baya da suka taba jagorantar kungiyar.
You must be logged in to post a comment Login