Kiwon Lafiya
Fadar shugaban kasa ta zargi ‘yan siyasa da shirya kashe-kashen manoma da makiyaya
Fadar shugaban kasa ta zargi ‘yan siyasa da shirya kashe-kashen da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya a yankin arewa maso tsakiyar kasar nan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar jiya a Abuja.
Sanarwar ta ce akwai wata kullalliya da wasu fusatattun ‘yan siyasa da sukayi wadaka da dukiyar kasar nan tsawon shekaru ke yi na neman raba kawunan al’ummar kasar nan wajen amfani da rikicin manoma da makiyaya.
Malam Garba Shehu ta cikin sanarwar dai, ya kuma ce; jami’an tsaro na aiki tukuru domin zakulo ‘yan siyasar da ke fakewa da makiyaya suna kashe mutane a kasar nan.
A cewar sanarwar kama wasu ‘yan ina da kisa da sojoji su ka yi a jihar Taraba a baya-bayan nan, ya nuna karara cewa ‘yan siyasa ne ke shirya kashe-kashen da ke gudana tsakanin manoma da makiyaya a yankin na arewa tsakiya.