Ƙetare
Faransa ta yi watsi da juyin mulkin Nijar
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce, kasar ba ta amince da ikirarin da dakarun sojin Nijar suke yi ba na karbe Iko a kasar bayan hambarar da Gwamnatin Bazoum, inda tace haryanzu a bangaren ta Muhammed Bazoum din ne halastaccen shugaban Jamhuriyar Nijar.
A cewar Faransa Bazoum shine mutumin da al’umma Nijar suka zaba, a don haka tace basu amince da kifar da gwamanatin farar hula da sojin sukai ba, inda tabi sahun sauran kasashen Duniya na kiraye-kirayen ayi gaggawar mayar da kasar hannun farar hula.
You must be logged in to post a comment Login