Labarai
Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da cibiyoyin raba abinci mai gina jiki ga yara

Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da cibiyoyin rarraba abinci mai gina jiki ga kananan yara a kananan hukumomi 12 dake fadin jihar.
Gwamnan jihar Dikko Radda ne ya bayyana yayin bude guda cikin cibiyoyin a Baure da yamacin jiya lahadi.
A cewar sa wannan wani mataki ne na dakile yawon samun yara masu dauke da cutar tamowa a fadin jihar da gwamnatinsa ta bijiro dashi.
You must be logged in to post a comment Login