Labaran Wasanni
FIFA Ranking: Najeriya ta ci gaba da rike kambunta a Afrika da Duniya
Kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles ta ci gaba da rike matakin da take na 34 a jadawalin da hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ke fitarwa duk wata na kasashen da suka nuna bajinta.
A jiya Alhamis 16 ga watan Satumbar da muke ciki na shekarar 2021 hukumar ta FIFA ta fitar da jadawalin watan Satumba.
Kalubale ya hana ‘yan wasan Najeriya buga wasanni 100-Enyeama
A Afrika ma Najeriya ta ci gaba da rike matakin da take na 5, yayin da kasar Tunisia take a matki na 25 a Duniya ta 2 kuma a Afrika kasar Senegal ce ta 1 a Afrika ta kuma 20 a Duniya.
Najeriya dai ta yi kokari a watan Satumbar da muke ciki inda ta doke kasar Liberia da ci 2-0 da kasar Cape Verde da ci 2-1 a wasannin neman tikitin buga kofin Duniya da za’a gudanar a kasar Qatar a shekara mai kamawa ta 2022.
Kasar Algeria ce ta 3 a Afrika ta kuma 30 a Duniya sai kasar Morocco ta 4 a Afrika ta kuma 33 a Duniya.
Kasar Belgium ta ci gaba da rike matakin da take na 1 a Duniya sai dai kasar France mai rike da kofin Duniya ta koma mataki na 4 yayin da kasar Brazil ke a matsayin ta 2 sai kasar , England da take a matsayin ta 3 inda kasar Italy ke a matsayin ta 5 a Duniya.
You must be logged in to post a comment Login