Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Bamu cimma yarjejeniyar  daukar Salisu Yusuf ba-Surajo Jambul

Published

on

Mahukuntan kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars, sun musanta Labaran da ake yadawa na daukar Salisu Yusuf a matsayin sabon mai horar da tawagar.

Shugaban kungiyar Alhaji Surajo Shu’aibu Yahaya Jambul, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Rilwanu Idris Malikawa Garu , ya fitar mai dauke da sa hannun sa a ranar Alhamis 16 ga watan Satumbar shekarar 2021.

Kano Pillars ta dakatar da daukar sabon mai horar wa

“Tabbas Salisu Yusuf, ya nuna sha’awar sa ta aiki da Pillars sai dai komai sai Allah ya nufa”.

“Bari in fada muku bamu yi magana da Salisu Yusuf ba, amma muna cigaba da dubawa” inji Jambul.

Shugaban ya ce Kano Pillars tana yiwa Salisu Yusuf , fatan Alheri tun da ya ce zai cigaba da aiki da Enugu Rangers International FC.

Jambul, ya tabbatar da cewar nan ba dadewa ba kungiyar zata fitar da bayanan yadda zata samar da sabon mai horar wa ga tawagar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!