Labarai
FIFA ta ɗage wasannin share fagen halartar gasar cin ƙofin duniya ɓanbagen nahiyar afurka

Hukumar ƙwallon kafa ta duniya FIFA) ta ɗage wasannin share fagen halartar gasar cin ƙofin duniya ta shekarar 2022 ɓangaren nahiyar afurka wanda aka tsara tun farko za ayi a watan yunin bana.
A yanzu dai hukumar ta FIFA ta ce za ayi wasanne a watan Satumban bana sakamakon ci gaba da fama da ake yi da cutar corona.
Haka zalika FIFA ta kuma bayyana rashin kyawun filayen wasanni a matsayin daya daga cikin dalilan
Bugu da kari, hukumar FIFA ta kara da cewa a watan Satumba, Oktoba da kuma Nuwamba za a fafata a wasanni tsakanin kasashen nahiyar da ke son halartar gasar ta cin ƙofin duniya
You must be logged in to post a comment Login