Labaran Wasanni
FIFA za ta yi taro kan yiwuwar buga kofin Duniya duk bayan shekaru 2
Hukumar Kwallon kafa ta Duniya FIFA, na shirin gudanar da babban taro kan bukatar sauya buga gasar cin kofin Duniya duk bayan shekaru 2.
Taron dai za’a gudanar dashi a ranar 30 ga watan Satumbar shekarar da muke ciki ta 2021.
Akwai yiwuwar hana ‘yan wasan da ba a yiwa rigakafin Corona ba buga Kofin Duniya
Ana saran taron zai samu halartar manyan hukumomin Kwallon kafa na nahiyoyi 6 domin tattaunawa da kuma jin ra’ayinsu akan Shirin na hukumar ta FIFA da ke ciki da kalubale.
Tun da fari dai tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal , Arsene Wenger wanda shine shugaban bunkasa harkokin wasanni a hukumar ta FIFA ne ya bijiro da bukatar buga gasar duk bayan shekaru 2.
Sai dai tuni tsarin ya fara fuskantar suka daga hukumomin kwallon kafa na nahiyar kudancin Amurka wato CONMEBOL da kuma hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA.
“A shirye FIFA take wajen bada dama ga kowanne bangare don jin bahasinsa da Kuma duba shawarwari kowa domin bunkasa Kwallon kafa a fadin Duniya”. cewar sanarwar da FIFA ta fitar.
Ita dai gasar cin Kofin duniya ana gudanar da ita duk bayan shekaru 4 tun daga 1930.
Sai dai gasar bata gudana a shekarun 1942 da 1946 sakamakon yakin duniya na 2 da akai.
You must be logged in to post a comment Login