Manyan Labarai
Firaministan Sudan ya tsallake Rijiya da baya
Firaministan kasar Sudan Abdolla Hamdak, ya tsallake rijiya da baya, a wani yunkurin kisa da aka kai masa a yau din nan ta hanyar tada Bom a jerin gwanon motocin sa lokacin da yake tafiya zuwa ofishin sa da safiyar yau a birnin Khartoum.
Firaminista Hamdok, ya tabbatar da labarin afkuwar hakan ta shafin sadarwar sa na twitter, in da yace ‘ina nan lafiya cikin kwanciyar hankali bayan yunkurin harin na yau’.
أطمئن الشعب السوداني أنني بخير وصحة تامة. ما حدث لن يوقف مسيرة التغيير ولن يكون إلا دفقة إضافية في موج الثورة العاتي، فهذه الثورة محمية بسلميتها وكان مهرها دماء غالية بذلت من أجل غدٍ أفضل وسلام مستدام. pic.twitter.com/jBezmJKqsz
— Abdalla Hamdok (@SudanPMHamdok) March 9, 2020
Ya kara da cewa abinda ya faru ba zai sa suyi kasa a gwiwa ba wajen ganin an tabbatar da juyin juya hali da kasar ke bukata ba, sai ma dan ba da suka saka a halin yanzu.
Firaminista Hamdok, ya saka hotunan sa yana murmushi a ofishin sa jim kadan bayan komawar sa, tare da labarin talabijin din kasar ke gudanarwa na yunkurin kisan da akayi masa a yau din.
labarai masu alaka.
An zargi DPO da hannu wajen kisan kai
Kawo yanzu ba a samu kungiya ko wani wanda suka dau alhakin kai harin ba, wanda ya lalata motoci guda biyu tare da fasa gilasan wasu da dama daga cikin jerin gwannon motocin dake rufawa Firaminista Hamdok baya.
Ministan yada labarai na kasar ta Sudan, Falih Salih, a ce yanzu haka ana fadada bincike don gano su waye suka kitsa abun tare da kai harin da niyyar kashe shugaban.
Abdollah Hamdok, ya karbi jagorancin kasar ne bayan da doguwar zanga zanga, da ‘yan kasar suka shafe suna gudanarwa ta tafi da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar Al-Bashir, wanda sojoji suka hambarar da gwamnatin sa a watan Afrilun shekarar data gabata.
You must be logged in to post a comment Login