Kiwon Lafiya
Fiye da muslmi 500 ne suka taya mabiya addini Kirista murnar Kirisimeti a Kaduna
Fiye da muslimai dari 500 ne suka taya ‘yan uwa mabiya addinin Kirista murnar zagayuwar haihuwar Yesu-Al-Masihu a gidan Limamin Majami’ar Avabgelical Pasto Yohanna Burus dake jihar Kaduna, don wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma.
Daga cikin wadanda suka halacci taya murnar akwai matasa da limamai da mata da kungiyoyin kishin al’umma da amsu rike da masarautun gargajiya da suka fito daga jihohin yakin arewacin kasar nan.
Da yake jawabi a wajen limamin Yohanna Buru ya ce ya ji dadi matuka da yadda ‘yan uwa musulmai suka nuna cewa babu wani bambanci tsakanin su da ‘yan uwan su mabiya addinin Kiristanci.
Ya ce wannan ziyarar taya murnar zai sake karababa wanzar da zaman lafiya da kuma kara son juna a tsakanin mabiya addinai.
Kazalika da yake jawabi a yayin ziyarar taya murnar tsohon shugaban sashin nazari tsirai na kwalejin kimiyya da fasaaha ta jihar ta Kaduna, Dr, Yusuf Nadabo wanda kuma shi ne jaogran matasan ya sake jadada muhimmancin samar da zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai a kasar nan.