Labarai
Fiye da mutane 40,000 ne suka mutu a hatsarin mota cikin shekara 1- FRSC
Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Nijeriya FRSC ta ce, sama da mutum dubu 40 ne suka mutu cikin shekara guda sakamakon hadarurruka daban-daban a fadin kasar.
Babban jami’i a hukumar, Dauda Ali Biu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da makon kiyaye hadura na Duniya da ake gudanarwa a kowacce shekara.
Yayin kaddamar da makon kiyaye hadura da majalisar dinkin duniya ta ware daga ranar 15 zuwa 21 ga watan Mayun ko wacce shekara, Babban jami’in hukumar ta FRSC Malam Dauda Biu ya ce, raunikan da ake samu idan an yi hatsari shi ne ke janyo ajalin dubban mutane tare da jikkatar wasu.
Haka kuma ya kara da cewa, mutane miliyan daya da dubu dari uku ne ke rasa rayukan su yayin da wasu miliyan 50 kuma ke jikkata sakamakon hadari a fadin duniya.
Dauda Biu, ya kuma ce, akwai bukatar ci gaba da daukar matakan inganta hanyoyi domin kare rayukan mutane a fadin duniya.
Rahoton: Ummulkhairi Abubakar Ungogo
You must be logged in to post a comment Login