Manyan Labarai
Fiye da shaguna dubu biyar aka bar su kara zube a kasuwanni – KAROTA
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta kammala dukkanin shirye-shirye don kai samame wuraren da ‘yan kasuwa ke kasa kaya akan titina ba bisa ka’ida ba, da basu dace ba a cikin birnin Kano da kewaye.
Shugaban hukumar ta KAROTA Alhaji Baffa Dan-Agundi ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyarar aiki wuraren da abun ya shafa a jiya Alhamis.
Baffa Dan-Agundi ya ce akan haka ne hukumar sa ta kafa kwamitin kar takwana don aiwatar da aikin, ya yin da y ace fiye da shaguna dubu biyar ne aka bar su kara zube a cikin kasuwanni daban-daban a nan Kano.
Daga cikin kasuwanni akwai na Sabuwar Tashar da Kwanar Ungoggo da Koafar Ruwa da yankin masana’antu na unguwar Nassarawa da kasuwar Sabon Gari.
You must be logged in to post a comment Login