Connect with us

Labarai

Adadin hadurran mota ya ragu da kashi 27 cikin 100 a bukukuwan Babbar Sallah – FRSC

Published

on

Hukumar Kiyaye afkuwar Haddura ta Kasa  FRSC ta ce adadin hadurran mota ya ragu da kashi 27 cikin 100 a lokacin bukukuwan Babbar Sallah na shekarar 2026 idan aka kwatanta da shekarar 2025.

Mai magana da yawun hukumar, Osondu Ohaeri, ya ce rahoton sintirin musamman na Sallah ya nuna cewa an samu hadurra 142 a bana, sabanin hadurra 191 da aka samu a bara. Haka kuma adadin mutanen da hadurran suka rutsa da su ya ragu daga mutum 1,364 zuwa 1,064.

FRSC ta danganta wannan nasara da karin sintiri a manyan hanyoyi, wayar da kan jama’a, tsaurara doka da kuma gaggawar kai dauki. 

Hukumar ta kuma bukaci masu amfani da hanyoyi su ci gaba da bin dokokin tuki domin rage hadurra a fadin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!