Connect with us

Labarai

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta gargadi gwamnatin tarayya kan tsaron ma’aikatan lafiya

Published

on

Ƙungiyar likitoci  masu neman ƙwarewa ta kasa (NARD) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 da ta fara aiwatar da tsarin kasa na kare ma’aikatan lafiya daga hare-hare sakamakon ƙaruwar cin zarafi da farmaki da ake kai wa likitoci a faɗin ƙasar.

 

Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai bayan kammala babban taronta na  da aka gudanar a Kano.

 

Haka kuma ta ayyana rikicin kwadago da gwamnati kan wasu bukatu 14 da har yanzu ba a warware ba a bangaren lafiya.

 

Shugaban NARD, Mohammad Suleiman, ya ce yawaitar hare-hare da tsoratarwa da cin zarafi da kuma amfani da karfi kan likitoci na barazana ga tsarin kiwon lafiyar Najeriya wanda tuni yake fuskantar ƙalubale.

 

NARD ta kuma buƙaci gwamnati ta fara aiwatar da tsarin kariya da martani ga hare-haren da ake kai wa ma’aikatan lafiya tare da fara aiwatar da dokokin da za su magance matsalar cikin kwanaki 21, ko ta Tsunduma ya jin aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!