Labaran Kano
Gamayyar kungiyoyin kwadago ta yi barazar gurfanar da Ganduje a Kotu
Kungiyar Kwadago reshen jihar Kano ta yi barazar gurfanar da gwamnan jihar Abdullahi Dr Abdullahi Umar Ganduje a gaban Kotu mudin bata dakatar da zaftari albashin ‘Yan fansho da ma’aikata ba.
Shugaban kungiyar Kwadagon ta jihar Kano Kwamarede Kabiru Ado Minjibiri ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da ya gudana da yammacin jiya Juma’a.
Kabiru Ado Minjibirin ya ce kungiyar ba zata lamunci matakin gwamnatin Kano ba na soke sabon tsarin mafi karancin albashi na ma’aikata wato Naira dubu 30 ba, kasancewar kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar sai da murho 3 suka zauna suka yanke wannan shawarar.
Shugaban kungiyar ya ce kungiyar na tunatar da gwamnatin Kano ta sani cewa, maganar albashi da fasnho hakki ne ba alfarma ba, “A don haka ba yadda za’a yi mutum daya zai zauna ya yi yadda yake so akan hakkin mutane”
Kafin sanarwar dai gwamnatin ta Kano ta yi Amai ta lashe kan soke amafani da sabon mafi karancin albashin na Naira dubu 30 ya yin da za’a koma kan tsohon na Naira dubu 18.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa zata cigaba da aiwatar da sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata a cikin wata sanarwa da kwamshinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar.
You must be logged in to post a comment Login