Labaran Wasanni
Gambo Muhammad ya dawo Kano Pillars a matsayin mataimakin mai horarwa
Tsohon dan wasan gaba na kasa Najeriya da Kano Pillars Gambo Muhammad ya zama mataimakin mai horarwa a tawagar Sai Masu Gida.
Gambo Muhammad ya koma Pillars ne bayan kammala karatun aikin horarwa a kwalejin harkokin wasanni ta kasa da ke birnin tarayya Abujua.
Tsohon dan wasan zakarun gasar Firimiya ta kasa har sau hudu zai kasance da Pillars har nan da lokaci masu yawa a nan gaba.
Mai magana da yawun kungiyar Rilwanu Idris Malikawa Garu ne ya sanar da hakan, gabannin wasan da Pillars zatayi da Plateau United a gasar NFPL.
Wanda hakan zai bashi damar kasancewa a matsayin mataimakin mai horarwa mai jiran kota kwana a wasan na Plateau da Pillars a wasan mako na 12.
Gambo Muhammad dai ya shafe shekaru da dama a matsayin dan wasa a Kano Pillars FC, inda ya jagoranci tawagar lashe gasar firimiya har hudu, kafin daga bisani ya koma Katsina Utd wanda ya shafe kakar wasanni biyu a can.
Jim kadan bayan amincewa da aiki a tawagar ta Kano Pillars Gambo Muhammad ya godewa shugaban kungiyar Surajo Shuaibu Jambul, wanda ya yi alkarin zai bada gudun mawa domin ci gaban kungiyar.
You must be logged in to post a comment Login