Coronavirus
Ganduje ya amince a rika bude mayankar “Abbatuwa” a ranakun sararawa

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da arika bude mayankar Abbatuwa a ranakun Litinin da Alhamis da ake sassauta dokar kulle a jihar.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake kaddamar da rabon tallafin takunkumin rufe baki da hanci miliyan biyu ga al’umma.
Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta rawaito mana cewa gwamna Ganduje yace za a rika bude mayankar Abbatuwan ne duba da yadda ake samun rashin tsafta a unguwanni sanadiyyar yanka dabbobi.
Karin labarai:
Ganduje ya kaddamar da rabon “Face Mask” miliyan biyu ga Kanawa
Covid-19: Sanya “Face Mask” ya zama dole a Kano
You must be logged in to post a comment Login